KWAZAZZABON YARKWANDO DUGABAU
Labari na gaskiya dangane da Kwazazzabon 'Yar Kwando da kuma saukar Shehu Mujaddadi a K'asar Dugabau.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Hakika Labarin da ake fada dangane da kwazazzabon 'yar kwando gaskiya ne. Ita 'yar kwandon ai aljana ce, watakila tana cikin jinsin fararen aljannu don kuwa bamu samu labarin wani data tab'a cutarwa ba.
Amma dai mutanen Dugabau dake k'asar Kabo ta jihar Kano sun bada shaidar cewa ana yawan had'uwa da Aljanna 'yarkwando a daf da wannan kwazazzabon.
Akwai wanda yace min takan fito da sigar tsohuwa ko Budurwa, har ma zata iya neman wani taimako daga gareka, ko kaganta tana wani uzuri nata, amma dai ba zata yarda kaga fuskar taba.
Ance ta tab'a fitowa wani mutum a siffar tsohuwa, sai tace masa ya taimaka ya tsallakar da ita ta haye ruwa, amma sai mutumin yak'I. Juyawar da zaiyi sai hangota yayi kanta a cikin ruwa, k'afufuwanta suna kad'awa a sama, a haka ta tsallake ruwan.
Wani mutum kuma mai noman rani a daf da wannan kwazazzabo ya shaida min cewa suna yawan ganin abubuwan mamaki dangane da aljanna 'yarkwando. Har yace min ba'a yi musu satar amfanin gona, domin kuwa ita aljanar ke musu gadi, sannan kuma yace gidan ta yana kusa da wani k'aton rimi da aka sare acan kan tudu idan an haye ruwa, ragowar surkukin kuma na d'auke ne da gidajen 'ya'yanta.
Shidai wannan kwazazzabo da ake kira 'kwazazzabon 'yarkwando' a kusa da garin Dugabau din yake, waje ne mai girman gaske dake hayin k'orama, yana da tarihi kuma, domin kuwa anan ne akace Shehu Usmanu Bn Fodio (Allah yajikan sa da rahama) ya taba sauka a sa'ar da yake yak'in Jihadi a k'asar hausa (wajajen 1804).
Marubuci Ibrahim Bala Gwarzo ya ruwaito a littafinsa 'Mazan kwarai' cewa a wannan wuri mai suna kwazazzabon Yarkwando Shehu Usmanu ya sauka ya huta ya kuma k'ara k'arfin rundunar sa. Daga nan ya afkawa masarautar Karaye da yak'i, sannan ya afkawa birnin kano.
Tarihi ya tabbatar mana da cewa Shehu Usmanu Danfodio ya sauka a wannan yanki na Dugabau, tunda akwai masallacin da shehun ya bud'e wanda akace wani mutum mai suna Isyaka ne ya gina shi acikin garin na Dugabau. Kuma sama da shekaru d'ari da tamanin, wannan masallaci ne babba a yankin, saboda an gina shi ya ginu, an kuma k'awata shi da ado dai-dai da wayewar maginan k'asa na wancan zamani.
Na tambayi wani Tsoho akan ko zamu samu wata shaida takamaimiya kamar misalin Littafi Alkur'ani maigirma, takobi ko wani abu wanda ya fito daga shehu mujaddadi a halin saukar sa a wannan yanki wanda kuma zai k'ara tabbatar mana da cewa shehu usmanu ya sauka a wannan guri?.. Sai dai hakan bai samu ba, watakila saboda jimawar zamani ko kuma gushewar Dattijan da suka kiyaye ainihin abinda ya faru a wancan zamanin gwargwadon yadda suka samu labari, amma dai ya tabbatar min da ingancin wannan labari, ya kuma k'aramin da cewa akwai wata Katuwar kuka mai suna 'JARMA' (wadda a yanzu ta fadi da kanta) dake daura da kwazazzabon 'yarkwando, itama ada can jarumai da sarakunan kasar Katsina na sauka a wurinta kafin su riski birnin Kano don kai harin yak'i ko aiwatar da wata buk'ata tasu.
Shikuwa kwazazzabon 'yarkwando, watakila k'oramar dake gudana adaf dashi ke jan ra'ayin matafiya masu shigewa daga k'asar katsina, sokoto da sauran wurare su yada zango a wajen. Tunda wani tsoho ya k'ara min da cewa ada, wajen mad'eba ce, watau ya tab'a zamowa dandali wanda masu sana'ar Su suka kakkafa rumfuna suke kuma dururuwar zuwa don kamun kifi.
Zuwa yanzu dai, Bamu san alak'ar wannan aljana da wadancan matafiya ba, ma'ana, tun a wancan zamanin an san da ita ko kuwa daga baya ne labarinta ya fito?, sannan idan akwaita wanne taimako ko akasarin haka ta basu?, to amma dai ko yanzu mun kara sanin d'aya daga manyan hanyoyin da matafiya kebi daga kano zuwa katsina ko Sokoto ada. Don haka munayiwa Allah godiya domin kuwa hakika ko yanzu mun k'ara Sani..
# SadiqTukurGwarzo
Comments
Post a Comment